Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kungiyance Akwai Matakai da aka Dauka


Wasu matasa 'yan banga
Wasu matasa 'yan banga

Biyo bayan dage babban zabe a Najeriya, da aka yi, kungiyoyi da masu fada a ji na kara wayar da kan matasa akan muhimmancin kada kuri’a.

Shugaban kungiyar muryoyi ta kasa, comrade Haruna Ayagi, shima ya ja hankalin matasa game da zabe ya kuma fadi cewa a karkashin kungiyarsa suna da wasu kananan kungiyoyi guda uku dake kula da yadda za a bada katin zabe na din-din-din, da kuma wadanda za a ba. Comrade Ayagi yace dage baban zaben da akayi ya tunzura mutane, suna ganin kamar za a kwace masu damarsu ne.

A kungiyance akwai matakai da aka dauka wadanda suka hada da bada hakuri ga al’umma saboda dage zaben da akayi, da kuma fadakar da matasa da iyaye, da kakanni akan muhimmancin karbar katinsu na din-din-din ga wadanda basu karba ba, wadanda suka karba kuma su kara inganta shi har zuwa lokacin zabe don ta haka ne kawai mutum zai iya yin zabe, ya kuma zabi abinda ranshi ke so. Bayan haka kuma ana kara wayar wa jama’a, kai akan cewa tada zaune tsaye don mutum bai sami abinda yake so ba to ba bashi ne mafita ba, a ta bakin Comrade Ayagi.

shugaban ya kuma ce dage zaben da aka yi ya sa sun kara zage dantse wajen wayar da kan matasa game da daukar makamai lokacin zabe, ganin yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da su wajen daukar masu makamai lokacin yakin neman zabe. Hakan ya sa mataimakin Speta –Janar din ‘yan sanda na kasa shiya ta daya ta Kano, yace zai dauki mataki akan duk wani dan siyasa da yake yawo da wadanda ke yawo da makamai. Abin duba wa anan shine babu daya daga cikin dangi ko ‘yayan wadannan ‘yan siyasar dake daukar makamai. Don haka matasa ku guji daukar makamai da zumman bin wani dan siyasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG