Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.
Ya ce rundunar ta sami labarin ne a ranar uku ga watan Oktoba cewa ana zargin wata mace da sassare ‘ya’yanta biyu da adda har lahira.
DSP Haruna, ya ce bayyana sunayen yaran da aka kashe da Irfan Ibrahim mai shekaru shida da kuma Zuhra Ibrahim mai shekaru uku.
Ya ce da ‘yan sanda suka sami labarin ba su yi wata-wata ba suka tura jami’ansu wurin kuma suka samu yaran da yankan wuka a jikinsu.
DSP Haruna ya ce an garzaya da yaran zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad a Kano inda likitcocin dake aiki a lokacin suka tabbatar da mutuwarsu.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda, Haruna, Hauwa da ake zarginta da aikata wannan danyen aikin ta kuma dabawa wata yarinya Aisha Abdullahi mai shekaru goma wuka, wadda ita kuma aka garzaya da ita asibitin koyarwan na Aminu Kano domin kula da lafiyarta.
Da take bada labarin yanda abin ya faru, Aisha Abdullahi, da ta shad a kyar ta ce bayan mijin Hauwa ya bar gida, yaranta suka yi fada a kan bindigar roba. Bayan ta kwace bundigar robar, sai tasa tabaryar karfe ta lalata bindigar robar, daga nan ne kuma ta kulle kofar gida ta fara kai hari a kan yaran.
Aisha ta ce "bayan ta sassare Zuhra (Beauty) da Irfan jinni ya zuba a jikin su kafin babban su ya shigo gida." Ta kuma ce an kwashe lokaci mai tsawo kafin aka kawo musu dauki lokacin yaran sun riga sun mutu.
Mahaifin yaran Mallam Ibrahim, ya ce matarsa "Hauwa ta fita daga cikin hayyacinta", saboda ya fahimci "ta fara wasu kalamam da mai hankali ba zai yi su ba"
A cewar mai Magana da yawun ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Habu Ahmad ya ba da umarnin mika batun ga bangaren kula da kisan kai na sashen binciken ‘yan sandan jihar Kano domin gudanar da binciken mai zurfi.
Facebook Forum