Watannin da aka kwashe ana zanga-zanga akan rikicin ‘yan ta’adda, tashin hankalin kabilanci da cin hanci da rashawa a kasar ne suka zafafa har sojoji 'yan tawaye suka kama shugaban kasar, suka kuma yi mashi juyin mulki a ranar 18 ga watan Agusta.
Wata kungiya da ake kira June 5 Movement ce ta jagoranci zanga-zangar, kuma wata sabuwar kungiya da ke kiran kanta Popular Movement of September 4 ta shirya wani gangami da aka yi a Bamako jiya Talata.
Bayan juyin mulkin, kwamitin sojan da ke mulki a kasar yayi alkawarin shirya sabon zabe, da farko sojojin sun ce zasu jagoranci kasar a matsayin gwamnatin rikon kwarya tsawon shekaru uku, daga nan a koma wa gwamnatin dimokradiyya, kafin daga baya suka rage lokacin zuwa shekara 2.
“Muna son sojojin sun jagoranci kasar a matsayin gwamnatin riko har lokacin da zasu dauka, a cewar Hamza Sangare, wani mai shago a lokacin da aka yi zanga zangar Bamako.
Facebook Forum