Shugaban hadakar kungiyoyin Alhaji Adamu, yace idan haka ta faru hakan zai shafi illahirin ‘yan kasar da tattalin arzikin Nijar baki daya.
Kungiyar ta bayyana matukar damuwa ainun game da yadda mambobinta suke kokawa a kan rashin aiki sakamakon yadda wasu takwarorin su daga kasashe makwabta suke kasha musu kasuwa a cikin gida da waje.
Shuwagabannin Kungiyar masu motocin sun ce wannan al’amari na yin barazana ga harkoki masu motocin. Shugabannin sun fada cewar motocin su na iya share watanni da dama basu samun aiki a kasashe kamar Togo, Ghana, Benin Cote d’Ivoire da sauransu.
Kungiyar masu motocin ta yi kira ga majalisar dokokin kasar jamhuriyar Nijer tayi watsi da sabon tsarin harajin da ake shirin soma azawa motocin dakon kaya a shekara mai zuwa bisa la’akari da yanda harkokin nasu ke huskantar barazanar durkushewa.
Facebook Forum