Kakakin sojin ruwan Najeriya Chris Eze Kobe yace 'yan Turkiyan da aka yi garkuwa dasu suna cikin wani jirgin ruwa mai dakon kaya ne a yankin Niger Delta..
Lamarin ya faru ne a daren Litinin amma har yanzu ba'a iya samun karin bayani ba daga kakain sojin.
Amma jami'an tsaron Najeriya na aiki da wasu jami'an kasa da kasa musamman hukumar Interpol domin ganin an sako wadanda aka yi garkuwa dasu.
To saidai jami'an jirgin ruwan na kasar Turkiya sun ce har yanzu ba'a tuntubesu ba akan lamarin jirginsu da ma'akatan.
Alhaji Dahiru Muhammad wani dan kasuwa mai safarar kaya zuwa kasashen ketare yace irin wannan lamarin ka iya kawo cikas ga yunkurin da kasar keyi na samo masu saka jari a kasar da kuma harkokin kasuwancin kasa da kasa..Idan 'yan kasuwa da masu saka jari suka ji ana yawan sace mutane a Najeriya zasu kauracewa kasar.
Mr. Dick Steven darakta a hukumar tsaron teku ta duniya dake da hedkwata a kasar Denmark yace jirgin ya taso ne daga Gabon akan hanyarsa ta zuwa Ivory Coast yayinda 'yan bindigan suka yi garkuwa da ma'aikatan jirgin.
Ga karin bayani.