Mai horas da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Massimiliano Allegri ya bayyana cewa rashin nasarar da kungiyartasa tayi a satin daya gabata cikin gasar Siria A mako na 28, ba rashin dan wasa Ronaldo bane kamar yadda wasu ke tunanin ba.
Kulob din Genoa ce ta doke Juventus da ci 2-0 a gasar ta kasar Italiya, wanda hakan ya kawo karshen jerin nasarorin wasannin da Juventus ke bugawa a bangaren lig na Itaty a bana.
Yayin wasan na ranar Lahadi, kocin Allegri, ya hutar da dan wasansa Cristiano Ronaldo, wanda ya ciwa kungiyar dukkanin kwallaye uku da ta lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai.
Sakamakon kin anfani da dan wasan a gasar Seria A wasu magoya bayan Juventus ke ganin ya taka rawa wajen rashin samun nasara a karawarsu Genoa.
Kungiyar ta Juventus ita take jagorantar gasar ta Seria A da maki 75, sai Napoli a matsayi na 2 da maki 60.
Bayan haka kuma har yanzu kungiyar tana cikin gasar kofin zakarun turai,
inda zata fafata da kungiyar Ajax a zagayen wasan daf da na kusa da na karshe Quarter Final.
Facebook Forum