Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Kano Ta Janye Nadin Wazirin Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Ranar Jumma'ar da ta gabata masarautar Kano ta sanar da nadin sabon wazirin Kano to amma jiya Talata ta janye nadin bisa ga rashin amincewar gwamnatin jihar.

Bayan ta sanarda nadin sabon waziri a makon jiya sai jiya Talata majalisar masarautar Kano ta janye nadin.

Alhaji Abbas Sanusi babban dan sarkin Kano kuma Wamban Kano yayi sanarwa jiya inda ya ce masarautar Kano ta zauna ranar Jumma'a ta nada sabon Waziri. Sai kuma ya cigaba da cewa majalisar ta zauna jiya ta janye nadin da tayi ranar Jumma'a.

Alhaji Abbas Sanusi yace janyewar ta biyo bayan rashin amincewar gwamnatin Kano ne da nadin da masarautar tayi. Yace yanzu an samu daidaito tsakanin majalisar sarkin Kano da gwamnatin Kano.Yace babu wani abu tsakanin masarautar da gwamnati.

Ranar Jumma'a da ta gabata masarautar ta sanar da nadin Malam Nasir Muhammed Nasir Limamin Masallacin Fagge dake Kano a matsayin sabon Wazirin Kano. Tshohon Wazirin Sheikh Isa Waziri ya rasu cikin watan azumin bara.

Dr Abdullahi Umar Ganduje mataimakin gwamnan Kano ya bayyana dalilin rashin amincewar gwamnati da nadin sabon Wazirin. Bangaren tsaro ya rubutowa gwamnati cewa mutane basu amince da nadin shi Malam Nasir ba. Sakamakon rahoton hukumar tsaro sai gwamnati ta tura wanda yake ba gwamna shawara akan masarautar Kano cewa kada su nada Malam Nasir. Sakon ya samesu amma basu janye ba.

Daga bisani kuma sai ga rahoto daga hukumar SSS cewa abun da ake son a yi zai kaiga rashin jin dadi ko lokacin da ake nada sarautar ko kuma nan gaba. Saboda haka hukumar ta ba gwamnati shawara a dakatar da bada sarautar.

Sabili da shawarar da hukumar tsaro ba bayar gwamnati ta rubuta wasika a janye bikin. Amma domin a tabbatar cewa masarautar ta samu wasikar sai gwamnan jihar yace mataimakinsa ya kai wasikar da kansa zuwa wurin sarkin Kano. Ya ga sarkin Kano ya kuma nuna masa rashin jin dadin abun da ya faru. Ya jaddadawa sarkin cewa gwamnati bata amince a yi bikin ba.

Amma da mataimakin gwamna ya isa wurin sarkin ya gaya masa cewa masarautar zata cigaba da nadin kuma gwamnati bata da izini tace ga wanda za'a nada. Yace yadda masarautar ta dauki maganar ba haka take ba. Idan gwamnati bata da hannu a lamarin menene yasa suka rubuto suna neman amincewar gwamnati.

Wannan shi ne karo na farko da majalisar masarautar Kano tayi amai ta kuma lashe lamarin da wasu ke ganin babban koma baya ne ga masarautar da kima da kuma martabar masarautar. Amma Wanban Kano Alhaji Abbas Sanusi bai yadda lamarin zai shafi martabar masarautar ba.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG