Gwamnatin shugaban Amurka Barack Obama, ta bada labarin Masar ta gabatar da tuhuma a hukumance kan Amurkawa da dama dangane da bincikenda Misran ta gudanar kan baiwa kungiyoyi masu zaman kansu a kasar kudade ta hanyoyi da suka saba doka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland, tace jiya laraba Masar ta gabatarwa Amurka takardun tuhuma, ta kara da cewa masu fassara suna aiki ka’in-da na’in domin fassara fiyeda shafi dari da aka rubuta cikin larabci, domin tantance wadanne Amurkawa ne ake tuhuma da kuma abinda ake zarginsu akai.
Ranar litinin masu bincike a Masar suka ce sun gabatar caji daban daban kan mutane 43 ‘yan kasashen waje da kuma ‘yan gwagwarmaya na kasar, ciki har da Amurkawa 19 da suke aiki da kungiyoyin raya jaririyar demokuradiyya a kasar.
PM kasar karkashin mulkin soja Kamal Ganzouri, ya fada jiya laraba cewa kasarsa ba zata yi watsi da hukunta mutanen ba duk da barazanar da wasu wakilan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa, idan Masar bata sassauto ba, hakan ka iya shafar tallafin dala milyan dubu daya da dari uku da Amurka take baiwa Masar ko wace shekara.