Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Na Harsashen Za'a Samu Karancin Ruwan Sama Bana


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Bisa ga harsashen da masana suka cewa za'a samu karancin ruwan sama bana yasa gwamnatocin arewa suna cigaba da jawo hankalin manoma domin su yi shuka da wuri.

Yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa Kaltungo gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya gargadi manoma su tashi tsaye su yi shuka da wuri domin koda ruwan sama zai tsaya ba zata.

Gwamnan ya fadawa manoma cewa gwamnatin jihar ta samarma manoma duk kayan da suke bukata domin su bunkasa aikin noma a jihar da nufin samun isasshen abinci. Yace su yi shuka da wuri domin sun samu rahoto cewa daminar bana ba zata dade ba.

Shi ma kwamishanan gona na jihar Yobe Adamu Garba Talba yace duk da matsalar tsaro da suke fuskanta yana da kwarin gwiwar za'a samu damina mai albarka bana. Gwamnatin jihar ta shirya domin jihar ta dogara ne akan noma inda fiye da kashi tamanin cikin dari na al'ummar jihar manoma ne. Kamar jihar Gombe sun tanadi taki da zasu raba.

Yau ne gwamnan Gombe zai kaddamar da sayar da taki ma manoma domin aikin gona na daminar bana.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu Muhammed.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG