Cibiyar Nazari da Binciken Tsaro ta Jamhuriyar Niger ta gudanar da wani taro domin samo hanyar yaki da masu anfani da hanyoyin sadarwan zamani don kawo wa tsaro cikas.
Cibiyar tace ta shirya taron ne domin musa’ayar ra’ayi tare da sanin hanyoyin da zasu bullo wa masu anfani da wannan hanyar domin cuta, danfara da yaudaran jama’ar kasa.
Mataimakin shugaban hukumar, AbdulAzeez Garba ya bada misali da kungiyar Boko Haram dake anfani da hanyar sadarwan zamani wajen barbaza akidojin su,
Yace taron zai nemo hanyoyin da za’a dakile irin wannan matsalar tare da cusa halin da’a ga masu anfani da hanyoyin sadarwan ta zamani.
Ga Sule Mummuni Barma da karin bayani.
Facebook Forum