Shugabannin manyan kamfanonin kasashen duniya sun yi kira da a kawo karshen kayyade tafiye-tafiyen masu dauke da kwayar cutar HIV.
Shugabanni sama da kamfanoni ishirin sun bayyanan yau Lahadi cewa, iyakar da aka yiwa kasashen duniya 46 ba wariya bane kadai, amma yana da illa ga harkokin kasuwanci. Sun bada sanarwar tasu ne, yayinda kimanin kwararrun binciken kwakwa dubu 25, da shugabannin siyasa da jami’an diplomasiya da kuma masu ruwa da tsaki suke fara taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa na kwana shida a Washington.
Shugaban kamfani tufafi na Levi Strauss, Chip Bergh ya bayyana cewa, a harkokin kasuwanci da ake neman yin fice, kamfanoni suna bukatar sukunin aikawa da ma’aikatansu duk wurin da ake bukatarsu.
Za a yi taron da aka saba gudanawar bayan kowacce shekar biyu ne a Amurka, karon farko cikin shekaru 22, bayanda shugaban Amurka Barack Obama ya dage dokar hana masu dauke da cutar kanjamau tafiya a shekara ta dubu biyu da goma.