Manoma a kasar Kenya na sa ran cin moriyar wani shiri na bada bashi mai inshora da zai taimaka mu su wajen sayen kayan aiki da irin shuka. Ba kamar sauran basussukan banki ba, wannan tsarin bashin da ake kira Risk Contingent Credit Scheme da turanci, wanda ke zaman bangaren wani shiri na cibiyar binciken manufofi akan abince ta kasa da kasa da ake kira IFPRI a takaice, mai mazauni a birnin Washington, an yi shi ne da zummar samawa manoma sauki daga asarar da suka yi a kakar noma sakamakon rashin kyaun amfanin gona saboda canjin yanayi.
Yanzu kakar damina hudu Kenan, garin Machakos ke fama da karancin ruwan sama kuma a haka manoma suke kallo gonakin su su na lallacewa. Sauyin yanayi na gab da jefa su cikin talauci domin maimakon su ciyar da iyalan su da abincin da suke nomawa, sai dai su shiga kasuwa su sayi abincin da za su ci.
Gab da sake aukuwar wani fari a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai (2017) aka fito da wani shiri na agaji wanda ake bada bashi mai suna “Risk Contingent Scheme da turanci. Kwararre a fannin kimiya, Linzhou ne ke jagorantar shirin.
"Idan damina ba ta yi kyau ba, baza a bukaci manoma su biya bashin da aka basu ba. Amma kuma, idan damina tayi kyau ya zama wajibi manoma su biya bassusukan da aka basu da kudin inshorar, a cewar Linzhou.
Yanzu haka shirin yana matsayin gwaji ne, amma an sa ran za a fito da shi a a sauran kasashen Afirka masu fama da karancin ruwan sama.
Facebook Forum