Za a gudanar da taron a Kaduna domin fahimtar juna tsakanin yankunan biyu bisa dagewa da masu rajin kafa kasar Biafra keyi da kuma wa’adin sallamar ‘yan kabilar Igbo daga Arewa da wasu kungiyoyi suka bayar.
A tattaunawa da wakilin sashen Hausa, Nasiru El Hikaya, Manjo Al’mustafa yace fahintar juna ta zame wajibi, domin akwai sa bakin wasu, wadanda basu son zaman lafiya a cikin lamarin, wanda idan anyi sake hakan ka iya haifar da fitina.
Manjo Al’mustafa wanda ya bada musali da yadda fitina ta gallabi kasar Libya da Sham da Yaman, yace Najeriya ta gaji da fitina tun yakin basasa.
Kuma gashi yanzu da kyar aka samu rage kaifin boko haram.
Facebook Forum