Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Paris-saint German Thomas Tuchel ya bayyana cewar ficewar su daga gasar cin kofin zakarun turai zaluncine, lura da cewa, a minti na 94 aka fidda su daga wasn.
Na’urar taimaka wa alkalin wasa ta VAR ta ba Manchester United bugun daga kai sai gola da ake kira Penalty da turanci, bayan kwallon da dan wasan Manchester united Diogo Dalot, ya buga ta sami hannun Presnel Kimpembe a da’irar ragar PSG. Ko da yake kocin bai fito karara wajen sukar alkalan da suka jagoranci wasan na ranar laraba da ta wuce ba.
Shi kuwa dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, da bai sami damar buga wasan ba saboda jinyar kafar sa da ya kwashe tsawon makonni 10 yana yi, ya bayyana bugun daga kai sai gola a matsayin abin kunya, yana mai cewa kwallon ta samu Kimpembe a bayansa ne ba hannunsa ba kamar yadda na'urar bidiyo ya nuna.
Bayan haka Neymar ya alakanta alkalan da suka jagoranci wasan da rashin sanin aiki.
Manchester United ta samu nasara da ci 3-1, a wasa na biyu inda jimlar wasan ya zama 3-3, lura da cewa, PSG ta doke Manchester United da ci 2-0 a karawarsu ta farko da suka yi a filin wasan Old Trafford a ranar laraba.
Manchester United ta samu nasara ne sakamakon yawan kwallayen da ta zura a gidan PSG a Paris har guda 3.
Marcus Rashford ne ya jefa kwallon a bugun daga kai sai gola da ya zo a kurarren lokaci, yayin da Romelu Lukaku ya zura sauran kwallayen biyu. Ita ko PSG ta samu damar jefa kwallo daya ne daga dan wasanta Bern.
Facebook Forum