Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na iya rasa 'yan wasanta guda shida a karshen kakar wasa ta bana, uku daga cikinsu akwai Ander Herrera, Juan Mata da kuma Alexis Sanchez.
Kocin kungiyar Ole Solskjaer na duba yuwar sayar da Sanchez, amma saboda girman albashin da dan wasan ke karba na iya dakatar da masu
zawarcinsa.
Sai dai kuma kungiyar tana kan tattaunawa da Herrera da Mata, wanda yarjejiniyar kwamtiraginsu zai kare a karshen kakar wasa ta bana.
Wasu rahotanni na cewar Ander Herrera, yacinma wata kwarya kwaryar yarjejiniya da PSG, kan komawar sa kulob din sai dai babu wani tabbacin haka daga mahukunta a kungiyar ko wakilansa.
Shi kuwa Sanchez wasanni biyar kacal ya fara bugawa, inda ya shiga canji a minti shida, yaci kwallo daya tun bayan da Ole Gunner Solskjaer, ya karbi ragamar kungiyar daga hanun Jose Mourinho, cikin watan Disamba 2018, amman yana daukar albashi mafi tsoka a kungiyar inda ya ke karban fam dubu £391,000 duk sati da karin £75,000 a duk wasan da ya buga.
Duk da haka akwai kungiyoyi da ake ganin za su iya biyan albashin nasa, sai dai ba a san wacce ce ba, musamman ganin yadda tauraruwarsa bata haskakawa tun bayan barinsa Arsenal a Janairun 2018.
Rabon 'yan wasa su fita daga kungiyar masu yawa haka tun a shekarar 2015, lokacin da Louis van Gaal, ya sayar da 'yan wasa shida, wadanda suka hada da Di Maria, Tom Cleverley, da Anders Lindegaard.
Facebook Forum