Malasia tace ta amince Amurka taci gaba da neman jirgin nan nata da ya bace a shekarar 2014 mai lamba 370.
Ministan sufuri na kasar Liow Tiong Lai ya fada yau asabar cewa kanfanin dake wannan aikin zaici gaba da aiki.
Kanfanin zaici gaba da aikin ne akan yarjejeniyar na, sai ya gano jirgin ne za a biya shi, amma idan bai gano kome ba to ba za a bashi ko sisin kwabo ba.
Ministan yace hakkin gwamnati ne ta bada amsar inda wannan jirgin yake.
Idan dai ba a manta ba wannan jirgin kirar 777 ya bace ne akan hanyar sa ta Kuala lumpa zuwa Beijing dauke da fasinjoji 239, kuma tun sailin da yayi batan dabo kawo yanzu ba labari.
Gwamnatocin Malasia,China, da Australia sun dakatar da aikin binciken wannan jirgin a cikin shekarar data gabata na 2017.
Sai dai kanfanin na Ocean Infinity na Amurka da yake ci gaba da wannan aikin binciken ya fada yau asabar cewa tuni jirgin sa ya fara wani sabon lalube.
Domin anfani da damar wannan yanayi a inda ake neman jirgin domin ganin ko zai iya gano shi.
Facebook Forum