Dubban masu zaman makoki ciki har da Farai Ministan Iraqi Adel Abdel Mahdi da yau Asabar sun halarci shirye-shiryen jana'izar babban kwamandan zaratan sojojin juyin-juya hali na Iran, Qassem Soleimani da kwamandan sojin Iraqi Abu Mahdi al-Muhandis da kuma shugabannin sojojin Iraqi takwas wadanda suka mutu ranar Juma’a a harin da Amurka ta kai ta sama filin jiragen Baghdad.
Soleiman dai shine aka auna a harin da Amurka ta kaddamar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ne ya bayar da izinin harin kan Soleimani domin ya dakatar da wasu hare-hare da ya ce shi Soleimani din ke shiryawa kan Amurkawa dake yankin.
Dayawa daga cikin masu zaman makokin yau Asabar sun saka bakaken kaya ne, kuma suna dauke da tutocin kasar Iraqi da ta sojojin juyin-juya halin da Iran ke marawa baya. Wasunsu na kiran “Mutawa ga Amurkawa”
Iran dai ta yi alkawarin mayar da martani, lamarin da ya sa shugabannin duniya ke kira da a kwantar da hankali, wadanda ke tsoron yaki kan iya barkewa a yankin.
Facebook Forum