Mai horar da ‘yan wasan Super Eagles, Gernot Rohr, ya ce maki goma sha daya kacal ne Najeriya, ke bukata da zai bata damar samun gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya wanda za’a gudanar a kasar Rasha a shekara 2018.
Gernot, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai, ya ce yana tsammanin cewa maki goma sha daya Najeriya, ke bukata ta kasance ta farko a rukuninsu koda yake a cewarsa kowace kungiyar nada damar samun gurbi.
Najeriya ta fara fafutukar neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa karo na shida da doke kasar Zambia a gidanta da kwallaye biyu da daya a ranarlahadin da ta gabata.
A yanzu haka Najeriya, ke sama a rukuninsu da maki ukku, bayan da Algeria tayi kunnen doki da kasar Kamaru.
Mun san cewa abune mai wuya a wasan farko kungiyar tayi nasara kuma ba’a gidanta ba, yana mai cewa akwai gyaran da za’a yi gabani wasan su da kasar Algeria.