Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majiyoyi Na Zargin Cewa Mutane Sama Da 800 Ne Su Ka Mutu A Harin Boko Haram Kan Fotokol Ranar Laraba


Wasu jeragen yaki kenan a Fotokol bayan harin da 'yan Boko Haram su ka kai.
Wasu jeragen yaki kenan a Fotokol bayan harin da 'yan Boko Haram su ka kai.

Majiyoyi na kara tabbatar da cewa daruruwan mutane sun mutu a harin da Boko Haram ta kai Fotokol

Wani tsohon babban jami’in ‘yan sanda, wanda aka tuntuba a garin Fotokol da ke kasar Kamaru, y ace mutane akalla 800 ne aka kashe ranar Labara, bayan da ‘yan Boko Haram su ka ketara kan iyaka daga Nijeriya su ka kai hari. “Kusan Mutane 800 ne su ka mutu,” in ji Muhammad Gueyme, wanda ya bayyana hakan ta wata hirar da Sashin Faransanci na Muryar Amurka ya yi da shi. Ya kara da cewa mutane 100 ne su ka mutu a birnin. To amma ba a iya tantance wannan adadin ba.

Zuwa yau Alhamis ba a ma fara binne gawarwakin ba, a cewarsa. Kuma wai gawarwakin na yashe birjig a daji, wasu ma da nisan kilomita guda daga birnin.

Ana cikin wani mummunan hali a Fotokol, a cewar M. Gueyme, ta yadda har yanzu da dama daga cikin mazaunan wurin ke cigaba da kwanciya a daji saboda su na jin tsoron dawowa gida.

Mayakan Boko Haram sun abka ma masallacin birnin da misalign karfe 5:39 na safe lokacin an hallara don sallar asuba, inda su ka yi ta yanka fararen hula. Daga sai su ka juya kan sauran jama’ar gari, a cewarsa.

Yau Alhamis ma ba a ga sojoji na sintiri a garin na Fotokol ba, inji Gueyme.

Har yanzu dai ba a san sahihin adadin wadanda harin na Boko Haram ya rutsa da sub a. Wani shugaban kungiyar al’umma, wanda kafar labarai ta Reuters ta tuntuba a jiya Laraba y ace ‘yan Boko Haran din sun hallaka mutane sama da 100, ciki har da wadanda su ka hallakasu cikin masallatai da gidajensu.

A wata takardar da ya raba ma ‘yan jarida a yau Alhamis, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya y ace harin da aka kai ranar 4 ga watan Fabrairu ya yi sanadin mutuwar sojojin Chadi 13 sannan kuma 21 sun sami raunuka da kuma wasu sojojin Kamaru akalla 3 baya ga dinbin fararen hula.

XS
SM
MD
LG