Majalisar wakilan Najeriya ta rage shekaru biyar daga kowace kujera kamar yadda Onarebul Aminu Shagari yayi bayani.
Misali dan majalisar tarayya ya zamo shekara 25. Sanata ya zamao shekara 30 haka ma shugaban kasa ya zamo shekara 35.
Sun yi canjin ne domin a baiwa matasa suma su shiga a dama dasu. Dokar ta farantawa matasa rai kuma sun yaba.
Shugaban kungiyoyin hadakar matasan arewa Imrana Wadana yana mai cewa ba zasu kara yadda su zabi tsoho shugaban kasa ba saboda sun yi daya sun yi biyu basu samu fita ba.
Yanzu matashi zasu zaba wanda kuma bai yi daidai ba suna iya yi mashi kwarmato abun da ba zasu iya yiwa tsoho ba saboda shekarunsa.
Yace yanzu ba maganar jam'yyar suke yi ba. Duk matashin da ya cancanta zasu sa gaba.
Awal Lawal Uba yace yanzu suna bi jihohi jihohi suna hada kawunan matasa. Yace yanzu lokacinsu ne dattawa su rufa masu baya.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum