Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu Ta Soma Daukan Matakan Kwace Filaye


Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa wanda yake son ganin a sanke raba filayen kasar
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa wanda yake son ganin a sanke raba filayen kasar

Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu ta fara daukan matakan da zasu kaiga soma kwace filayen da fararen fata tsiraru suka mallaka ba tare da biyan diyya ba a lokacin da suke mulkin wariyar fata.

Majalisar dokokin Afrika ta Kudu ta dauki matakin farko na kafa dokar da zata ba gwamnati ikon kwace filayen da mutane suka mallaka ba tare da biyan diyya ba.

Burin da ake nema a cimma da wannan tsarin da jam’iyyar ANC mai mulki ta gabatar shi ne cike gibin dake akwai da ya durkusar da bakaken fatar kasar. Duk da yake tsarin ya sami gagarumin goyon baya, zai dauki lokaci kafin a iya aiwatar da shi.

Majalisar dokokin ta kada kuria ranar Talata kan yadda za a yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ya bada damar kwace filaye, abinda ya kwantawa al’ummar kasar da turawa tsirarru har yanzu suke iko da galibin gonaki a rai.

Sai dai dan siyasa mai ra’ayin mazan jiya Julius Malema, yace ba wani canjin a zo a gani da za a samu.

Injishi “Babu wanda zai rasa gidansa, babu wanda zai rasa masana’antarsa, abinda kawai muke cewa, shi ne, ba zasu mallaki kasar ba, za su yi haya ne, bisa ga shirin da aka yi musamman bayan yiwa kundin tsarin mulkin kasar garambawul”.

Jam’iyyar hamayya ta Democratic Alliance ta kada kuriar kin amincewa da matakin, ta kuma dora alhakin jinkirin sake raba gonaki kan jam’iyyar ANC wadda ke mulki a kasar tun bayan kawar da mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG