Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, zai yi wani taron gaggawa domin tattauna rikicin yammacin kasar Myanmar da ya-ki-ci-ya-ki cinyewa, wanda ya tilastawa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya dubu 370 ficewa zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da kasar.
A ranar Litinin, Burtaniya da Sweden suka nemi a gudanar da zaman, bayan da shugaban hukumar kare hakkin bil adama a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad al- Hussein, ya kwatanta yadda ake daukan ‘yan kabilar ta Rohingya a matsayin “wani littafi da ke nuna misalin kisan kare dangi.”
Zeid ya fadawa Majalisar ta kare hakkin bil adama a Geneve cewa, ofishinsa ya samu rahotanni da dama da kuma hotunan da tauraron dan adam ke dauka, wadanda suka nuna yadda jami’an tsaron kasar da mayakan sa kai ke aikata kisan gilla tare da kona kauyukan Rohingya a jihar Rakhine da ke kasar ta Myanmar.
Har ila yau, Zeid ya kawo misalai da wasu rahotanni da ke nuna yadda dakarun Myanmar ke binne nakiyoyi akan iyakar kasar da Bangladesh.
Yayin da take magana a Bangladesh, Darektar da ke sa ido kan rikice-rikicen dake aukuwa, ta kungiyar Amnesty International, Tirana Hassan, ta fadawa manema labarai cewa, “’Yan kabilar ta Rohingya sun kwashe kwanaki suna tafiya da kafa, domin gujewa abinda za a iya kwatantawa a matsayin ayyukan cin zarafin bil ‘adama da aka shirya.”
Facebook Forum