Domin kaucewa mummunan tashin hankalin da zai fuskanci al’umma, Majalisar Dinkin Duniya na kira da a kara habaka taimakon jin kai zuwa Somaliya. Yankunan da suka fi kowanne yankuna shiga cikin wannan matsala a kasar Somaliya sune yankunan Bay da kuma Bakool a kudancin kasar. Sai kuma Sool da Sanaag da suka biyo bayansu a arewacin kasar.
Kamar yadda jami’an ayyukan jin kai suka bayyana, ance yanayin abin da ke faruwa a yankunan a iya kiran sa mafarin Faro. Wakilin hukumar UNICEF Steven Lauwerier ya ziyarci yankunan da suka fi shiga cikin wannan yanayi, inda ya bayyana cewa ya ga busassun gawarwakin dabbobi, ya kuma kara da cewa ya ga mutane sunyi asarar fiye da kaso 90 na amfanin gonar da suka noma sakamakon rashin ruwan sama na tsahon shekaru biyu.
Ya kara da cewa idan ba a dauki wani mataki yanzu ba, to mai yiwuwa a fuskanci yawan mace-mace na mata da yara mai muni. Hukumar mai asusun tallafin na yara na wato UNICEF da kuma cibiyar shirin ciyar da abinci ta WFP duk a karkashin Majalisar Dinkin Duniyar, sun bayyana cewa suna bukatar fiye da dalar Amurka Miliyan $450 a watanni masu zuwa domin kare farin.
Facebook Forum