Hukumar kula da ‘yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya yanzu haka tana rarraba kayan agaji ga wadaanda suka fi tagaiyyara a dalilin rikicin, sannan hukumar ta bada sanarwar cewa mutanen da yawansu ya kusa kaiwa miliyan biyar ne yanzu haka a Sudan ta kudu ke bukatar agaji matuka gaya.
Rikicin Kabilanci da rigimar da mayakan ‘yan tawaye keyi da sojin Gwamnati a Sudan ta janyo asarar rayukan Bil Adama masu tarin yawa sannan miliyoyin magidanta suna ci gaba da tagaiyyara. Yanzu haka mutane sama da dubu dari hudu ne suka tsere daga gidajensu zuwa kasashen dake Makwabtaka da Sudan.