Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Bita Kan Kare Mata a Nijar


 Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

A cigaba da gwagwarmayar kare mata da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin da ke hada kai da ita ke yi, an yi wata bita a Nijar kan makomar mata da kuma yadda ake musguna masu.

A wata hobbasa ta neman mafita kan yawan musguna ma mata a Janhuriyar Nijar, Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wani taron bita a Yamai, babban birnin kasar, inda sarakuna da shugabannin addinai da na kungiyoyi su ka samu halarta.

Manufar taron ita ce a yi musayar ra’ayi tsakanin mata da maza da shugabannin addinai da na kungiyoyi da kuma na jama’a kan hanyar da za a kawo karshen yawan cin zarafin mata a Janhuriyar ta Nijar.

Madam Kako Hajiya Fatima ta wata kungiyar gwagwarmaya ta mata ta ce zayyana nau’ukan cin zarafin mata da akan yi tare da shan alwashin cigaba da gwagwarmayar kawo karshensu. Ta ce akasari akan rabe ne da sunan hakkin aure a ika kunatata ma mata. Shi kuwa Usman Danbashi, shugaban wata kungiyar kare hakkin dana dam, ya ce rashin kawo karshen amfani da wasu dabi’u na tun zamanin jahiliyya na daga cikin dalilan cigaba da kwara da kuma kuntata ma mata da ake yi. Ya hatta macen da ba ta samun haihuwa ana kaskantar da ita tare kuma da gallaza ma ta. Sheikh Sani Sabi’u Suleiman wanda ya jagoranci malaman addinin Musulunci ya nesanta Musulunci daga duk wani nau’i na cutar da mata.

Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG