Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Kafa Kwamitin Binciken Hada-hada Da Kudin Bitcoin


BITCOINS
BITCOINS

Rashin tabbas da kushewar da Babban Bankin Najeriya yi yiwa kudin Bitcoin ya sa Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin binciken makomar wannan kudin da ake hada had- dashi ta yanar gizo da wasu lambobin sirri.

Majalisar Dattijan Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai duba tare da kuma gudanar da bincike akan hada hadar kudi na Bitcoin.

Yanzu haka dai Bitcoin na karbuwa tsakanin 'yan Najeriya lamarin da majalisar ta ce yana da hadari, musamman bayan da babban bankin kasar ya nisanta kansa da kudin..

Dr Dauda Muhammed Kontagora na Jami'ar Bayero ya yi karin haske akan wannan sabon kudin. Ya ce ba irin kudin da aka saba dashi ba ne. Ba takarda ba ne. Ana hada hada dashi ne ta yanar gizo tare da yin bayanan sirri ta yanar gizo da lambobi. A cewarsa a shekarar 2009 ne aka kirkiroshi. Har yanzu ba 'a san ainihin sunan wanda ya kirkiroshi ba amma ya sakaya da suna Sakamoshi Nakamoto.

Dr Kontagora ya kara da cewa matsalar kudin babu wani da yake tsakiya kamar dillali ko banki. Idan wata matsala ta faru babu wata hukuma ko gwamnati da zata taimaki mutum ya gano kudinsa.

Ahmed Usan Bala ya ce ya san batun Bitcoin amma shi bai taba hada-hada dashi ba. Ya ce ana anfani dashi ta yanar gizo sannan muggan mutane suna shiga harkar kudin.

A cewar Dr Kontagora kasashen duniya basu amince da Bitcoin ba kuma suna yiwa 'yan kasarsu gargadi su kauce masa. Har yanzu baya cikin hada hadar kudi na tattalin arziki

Ga rahoton Babanginda Jibrin

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG