A Najeriya, kwararru a fanin kimiyar siyasa da manyan a Siyasa sun fara mahawara akan batun kira da wani dan Jamiyyar APC yayi cewa, zai garzaya Kotu domin a tilasta wa Majalisar Dattawa ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin Shugaba Mohammadu Buhari ya zarce da mulki bayan ya kammalla wa'adinsa a shekarar 2023.
A wani mataki mai kaman mayarda martani, wasu 'yan Majalisar Dattawan Najeriya sun yi tsokaci akan wannan bukata ta Charles Oko, dan jamiiyar APC a Jihar Ebonyi da ke kudu maso kudanci Najeriya, inda ya ce yana so shugaba Buhari ya zarce da mulki. Sanata Abdullahi Adamu ya ce, wanan kira ba abu ne mai yiwuwa ba, domin ba yadda za a yi gyaran Kudin tsarin Mulkin kasa da ke dauke da mutane fiye da miliyan dari biyu domin mutum daya. Sanata Adamu ya kara da cewa ba a yin haka a siyasa, kuma wanan abun rudani ne kawai domin a tozarta wa yan Arewacin Najeriya da ita ma kanta Majalisar Dattawa da ake ganin tana zaman lafiya da bangaren shugaban kasa.
Shi ma Sanata mai Wakiltar Kaduna ta Arewa, Uba Sani ya ce, tuni shugaba Buhari ya yi wa tufkar hanci, inda ya fito bainar jama'a a babban taron Jamiyyar APC mai mulki ya ce, shi ba zai sake tsayawa takara a karo na uku ba. Sanata Sani ya ce, ga duk mai hankali ya kamata ya janye wannan magana a koma a dukufa wajen gina kasa domin al'umma su samu su mori demokradiya.
Amma ga Malami mai koyar da Kimiyar Siyasa a Jami'ar Baze a Abuja, wato Farfesa Usman Mohammed yana ganin akwai kanshin gaskiya a cikin wannan magana domin irin jituwar da ke faruwa tsakanin Majalisa da bangaren shugaban kasa a yanzu yana nuni da cewa wanan mataki yana cikin dalilin da ya sa aka matsa domin a zabi shugabanin da ke gudanar da Majalisar Kasa a yanzu.
A halin yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido, domin su ga yadda wannan maganar zarcewar Shugaba Buhari da mulki a karo na uku zata kaya.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda Daga Abuja, Najeriya:
Facebook Forum