Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci ma’aikatar kwadago da nagartar aiki ta kasar ta kafa kwamitin da zai sake yin nazari akan tsarin kayyade shekaru wajen daukar aiki, domin bai wa matasa da suka kammala karatu damar samun ayyukan yi.
Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wani kudiri da dan Majalisar Dattawa da ke wakiltar jihar Sokoto ta gabas Sanata Ibrahim Gobri ya gabatar inda ya nemi a sake yin nazari akan yadda hukumomin gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu suke kayyade shekaru na daukar ma’aikata, wanda hakan ke sa da dama daga cikin wadanda suke da takardun kammala karatu ba sa samun guraben aiki.
Sakamakon karuwar rashin ayyukan yi a Najeriya, da yawa daga cikin matasan da suka kammala karatun digiri kuma suka shafe shekaru da dama suna neman aiki, wasunsu sukan shiga aikata miyagun ayyuka da ke hura wutar tabarbarewar sha’anin tsaro a kasar a cewar Sanata Ibrahim Gobri.
Dakta Abdulhakeem Garba, na Kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kaduna ya ce ana rasa kwarraru da za su iya ba wa kasa gudunmowa sabili da shekarunsu sun zarta yadda doka ta tanadar.
Sai dai a na shi bangaren Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, kuma masanin harkokin shari’a, ya ce zai yi wuya a iya aiwatar da wannan kudiri duba da yadda ake sakaci da dokoki a Najeriya.
Abun jira a gani shi ne ko kwalliya za ta biya kudin sabulu, ganin cewa shugaban Majalisar Dokokin kasar Ahmad Ibrahim Lawal ya yi na’am da kudirin kana ya bukaci gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatar kwadago da nagartar aiki akan ta kafa kwamitin da zai sake yin nazari game da tsarin kayyade shekarun daukar aiki cikin gaggawa.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Facebook Forum