Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Hukuncin Kisa


 Majalisar Tarayyar Najeriya
Majalisar Tarayyar Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da ta gindaya hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da mutun har ya rasa ransa, babu tara babu beli.

Ganin yadda jama’a da dama ke fadawa cikin bakin cikin masu gaekuwa da mutane majalisar dattawa ta amince da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da aikata wannan mummunar dabia na yin garkuwa da mutane kama daga fasinja zuwa kananan da manyan mutane.

Wannan dabi’a dai ya addabi sassan kasar Najeriya, wanda alokuta da dama wadanda aka yi garkuwa dasu ke harasar dukiyoyi koda bashi ne domin samawa wadanda aka yi garkuwa dasu ‘yanci ko kuma a kubutar dasu.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai an kama tsopfaffin Ministoci da masu fada aji da kuma matasa har ma wasu suka rasa rayukansu.

Masu yekuwar kare hakin bil – Adam, sun kara jinjinawa matakin da majalisa ta dauka ya zuwa yanzu ma akwai jihohi dasuka rattaba hannu akan wannan doka kamar jihohin Legas da Abia da Edo da Akwa Ibom da Anambra da Ebonyi da Enugu da Rivers da kuma Imo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG