Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sauke Ibrahim Magu


EFCC: Ibrahim Magu a gaban Majalisar Dattawa ranar 03/15/2017
EFCC: Ibrahim Magu a gaban Majalisar Dattawa ranar 03/15/2017

Majalisar Dattawa ta sake aikawa Shugaba Mohammadu Buhari da umurnin ya sauke Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, tareda yin barazanar watsi da bukatar wanke duk wani jami'i na gwamnati da fadar shugaban kasa ta nemi a yi.

Duk da cewa an dauki lokaci ana kace nace a tsakanin bangaren zartaswa da na majalisar dattawa game da makomar mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa-EFCC, Ibrahim Magu, wannan sabuwar barazana ta bude wani sabon babi a kan al’amarin. A wani hukumcin da mai shari’a John Tsoho na kotun tarayya a Abuja ya yanke inda yace kashi biyu karamin kashi na ukua dokar shekara dubu biyu da hudu da ta kafa hukumar EFCC, ta ba majalisar dattawan hurumin zabar wanda zai shugabanci hukumar.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa, mai Magana da yawun majalisar dattijai Saneta Aliyu Sabbi Abdullahi, ya bayyana cewa, abinda ya janyo ja in ja da ake yi da fadar shugaban kasar shine, tsokacin da mai rikon shugaban kasa ya yi a baya cewa, ba lallai sai an kawo batun gaban majalisar dattawa ba, wannan ya haifar da muhawa a majalisa, suka kuma tsaida hukumcin cewa, wannan ba Magana ce da zasu dauka da wasa ba.

Ya bayyana cewa, majalisar tana bukata abi doka da ka’ida wajen zaben wanda zai rike wannan mukamin sabanin furucin mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibajo.

Kwararre a fannin kundin tsarin mulki Barrista Mainasara Kogo Ibrahim, ya bayyana cewa, tsarin mulki ya riga ya fayyace wannan batun a sashe na dari da talatin inda ya yi bayani cewa, shugaban kasa shine mai ikon zartas da al’amura na kasa, saboda haka dukan sassan mulki suna karkashinshi Domin haka yana da ikon zartas da duk abainda yaga zai kawo ci gaban kasa.

Saurari rahoton Madina Dauda domin karin bayani

Majalisa ta sake tada batun Ibrahim Magu-3:50"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG