To saidai yunkurin tsawaita kasafin kudin bana zuwa har watan Mayu na shekara mai zuwa bai kai majalisar dattawa ba inji Sanata Yusuf Abubakar.
Idan kuma an gabatar ma majalisar da bukatar Sanata Abubakar yace a doka majalisa na iya tsawaita wa'adin kasafin kudi. Yace ya san ana iya tsawaita kasafin kudi na watanni ukku. Bai sani ba ko doka ta tanadi tsawaita wa'adin kasafin kudi har na watanni shida.
Ta fannin shugaban kasa doka ta bashi ikon yin anfani da kasafin da wa'adinsa ya kare har na tsawon watanni shida kafin a yi wani. Ma'ana, shugaban kasa na iya cigaba da yin anfani da kasafin kudin shekarar 2016 har zuwa wani lokaci a shekara mai zuwa bayan da majalisa ta kammala aikinta a kan sabon kasafin.
Yanzu dai majalisar dattawa tana duba kwarya kwayar kasafin kudi na shekaru ukku masu zuwa kamar yadda doka ta tanada. Bayan sun gama ne shugaban kasa zai gabatar masu d kasafin kudin shekara mai zuwa.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.