Wani lauya mai rajin kare hakkin bil’adama a yankin Niger Delta Oweilaemi Pereotubo ya yi Allah wadai da cigaba da tsare wasu dalibai guda goma da jami’an sojojin Najeriya ke ci gaba da yi a yankin Gbramatu dake jihar Delta a wani yunkuri da sojojin suka yi na nema da kuma kama tsagerun Niger Delta dake fasa bututun mai a yankin, inda ya kira lamarin a matsayin take hakkin bil’adama.
Rahotanni sun bayyana cewa lauyan ya ce lamarin ya kasance abin damuwa matuka a yankin ganin yadda aka kama yaran aka garkame su tun watanni biyu da suka gabata a yayin da suke rubuta jarabawar kammala karatun sakandire kuma har yanzu babu tabbas akan tuhumar da ake masu.
Da yake Allha wadai da wani kamu da sojojin suka yi kwanakin nan, lauyan ya bayyana cewa ayyukan kame kamen matasan da sojojin ke yi a yankin ya saba ma doka, domin suna cin mutuncin jama’ar da basu jiba basu gani ba.
Daga karshe lauyan yayi kira da a saki daliban su goma, inda yace basu sami kammala jarabawar kammala makarantar sakandire da suke cikin rubutawa ba a lokacin da aka kama su.