Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwar Hagupit Na Cigaba Da Yin Barna A Kasar Filifinu


Guguwar Hagupit mai kadawa da karfi a kasar Filifinu
Guguwar Hagupit mai kadawa da karfi a kasar Filifinu

Bayan da mahaukaciyar guguwar 'hagupit' ta kusa gama kittawar da ta ke yi ta tsakiyar kasar Filifinu, hukumomi sun fara lissafin barnar da ta yi

Hukumomi a yankin tsakiyar kasar Filifinu sun fara kididdigar yawan barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Hagupit ta yi, wadda ta fantsamo a gabar gabashin kasar a jiya Asabar da iska mai gudun kilomita 210 a sa'a guda.

Mazauna tsibirin Samar da ke can lungu sun shafe tsawon dare cikin matukar firgici, su na da jin yadda iska da ruwan sama ke ta makar tagogi da gine-gine.

Wuta ta dauke a fadin yankin sannan kuma itatuwa da katakai sun fadi sun katse hanyoyi.

An yi hasashen cewa guguwar ta Hagupit za ta kada zuwa tsakiyar kasar ta Filifinu. An dai kwashe mutane kimanin 600,000 daga kauyukan da ke gabar teku da kuma wuraren da aka fai samun gocewar tudu.

Sojojin kasar na cikin shirin ko ta kwana don kai dauki a duk inda aka samu wata babbar matsala.

Masana ilimin yanayi sun ce guguwar ta Hagupit ita ce mahaukaciyar guguwa mafi karfi da ta addabi kasar ta Filifinu a wannan shekarar, to amma karfin na ta bai kai na guguwar Haiyan da ta auku a bara ba.

Waccan guguwar dai ta hallaka mutane sama da 7,300, ta kuma kado iska mafi karfi a tarihi zuwa doron kasa.

XS
SM
MD
LG