Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Ta Kashe Mutum Sama Da Dubu a Mozambik (Mozambique)


Barnar guguwar Mozambique
Barnar guguwar Mozambique

An tabbatar da aukuwar wani bala'i a Afurka, bayan da Shugaban kasar Mozambik, ya tabbatar cewa sama da mutum dubu sun mutu a kasar, bayan da wata mummunar guguwa dauke da ruwan sama ta ratsa ta kasar, a makon da ya gabata.

Shugaban kasar Mozambique, ya yi amannan cewa sama da mutum dubu sun mutu a kasar, bayan da wata mummunar guguwa dauke da ruwan sama ta ratsa ta kasar, wacce ke kudancin Afirka a makon da ya gabata.

Guguwar wacce aka yi wa lakabi da “Idai” ta fada yankin Beira, garin da ke kusa da Tekun Indiya mai tashar jiragen ruwa a gabar tekun kasar ta Mozambique a makon da ya gabata, inda ta yi tafiyar kusan kilomita 200 cikin sa’a guda.

Shugaban kasar ta Mozambique Filipe Nyusi, ya ce, a halin da ake ciki a yanzu, an tabbatar da mutuwar mutum TAMANIN DA HUDU, amma bayan da suka yi rangadin yankin da guguwar ta ratsa, sun fahimci cewa adadin mutanen da suka mutu zai iya kai wa dubu.

Ya ce “mun tanadi kayayyakin ceto mutane, kuma mun nemi taimako daga kawayenmu, sannan akwai likitoci da suke kan shigowa Maputo.”

Guguwar dai ta ratsa har cikin Zimbabwe da Malawi, inda ta zubar da ruwan saman da ya haifar da ambaliyar ruwa, wanda ya yi awon gaba da hanyoyi da gidaje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG