Jiya da misalin karfe bakwai na safe mazauna garin Biu suka soma jin karan tashin bamabamai da bindigogi lamarin da ya sa jama'a da dama suka firgita.
Jin karan fashewar bamabamai da bindigogi ya sa matasan garin suka yunkura domin kare garinsu. Sun yi kokari sun fatattaki maharan da ake zaton 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.
Maharan sun yi shirin kai hari a barikin sojoji dake cikin garin. Amma basu samu nasara ba sanadiyar jajircewar matasan garin da hadin gwiwar jami'an tsaro.
Bayanai na nuna cewa an fatattaki maharan kuma an kashe wasu cikinsu sakamakon kwantar bauna da sojoji suka yi masu lokacin da suke shirin kai hari kan barikinsu.
Wasu mazauna garin sun ce dama can sun ji labari maharan na shirin zuwa garin dalili ke nan matasan garin da sojoji basu yi barci ba. Saboda haka hanyar da suka bi suka shiga garin an yi masu kaca-kaca. Babu wanda ya tsere saidai wadanda basu riga sun shigo ba. An samu an kama wasu.
Nufin maharan shi ne su kama barikin sojoji inda kayan fada suke. Da zara sun samu nasara, kama garin gaba daya zai zama da sauki. To saidai mutanen garin sun yi ikirarin kashe maharan fiye da goma.
Duk da cewa wasu sun gudu zasu sake wani sabon shiri na sake kai hari a garin.
Ga karin bayani.