Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magungunan Jinya Da Ake Sayarwa Na Gurbatar da Ruwan Kogi


Taron masana a Austria
Taron masana a Austria

A wani taron masana ilimin kimiya a Austria an gano cewa magungunan jinya da ake sayarwa da mutane ke saya ba tare da izinin likitoci ba na gurbatar da ruwan kogi

Masana illimin kimiya sunce ruwan kogi da inda ake sarafa ruwa sun gurbace daga magungunan jinya da ake sayarwa, wadanda ake saye ba tare da izinin likita ba, kuma hakan yana jawo barazana ga yanayi da dabbobin daji.

Masana illimin kimiya dake wani taro a Vienna kasar Austria sunce idan ba’a dauki wani mataki ba, to matsalar zata karu da kashi sittin da biyar daga cikin dari nan da shekara ta dubu biyu da hamsin.

Magunguna sun hada dana jinyar ciwon jiki da magunguna makwafin ruwan kimiya da jiki ke samarwa ko fitarwa dake dora tasiri ga aikin wani farni na jiki da ake cewa hormones da turanci dake makamancin irin wadannan magunguna.

Yawancin wadannan magunguna suna bugewa ne cikin ruwan kogi ta baya da mutane da kuma dabbobi ke yi a saboda kadan daga cikin su ake tacewa a wuraren sarafa ruwa.

Masana daga Majalisar Dinkin Duniya sun ce kuma magunguna a cikin yanayi suna taimakawa wajen sa jiki bijirewa kaifin magunguna. Masana illimin kimiya sunce yanzu haka babu isasshen fasahar tinkarar wannan matsala a saboda haka ana bukatar rage dogaro akan irin wadannan magunguna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG