Ma’aikatan wata katafariyar gonar 'kokumba' mai suna "GreenHouse," da gwamnatin jahar Taraba ta yi sun gudanar da zanga-zanga saboda sallamarsu da gwamnatin jahar ta ce ta yi.
Ita dai gonar, wadda aka kashe kimanin Naira billion uku wajen yin ta za ta samar wa ‘yan jahar da gwamnatin karin kudaden shiga, to amma ma’aikatan dai na kokawa da shakulatin bangaro da su ke zargin an yi da su.
Wannan boren na zuwa ne a kusan kasa da makwanni biyu da ziyarar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya kai jahar Tarabar inda ko aka kai shi wannan katafariyar gonar kokumbar.
To sai dai tun ba’a je ko ina ba,tuni aikin ya soma fuskantar matsaloli musamman ta fuskacin ma’aikta da suke zargin shakulatin bangaro da kuma nuna sonkai.
Ma’aikatan dai sun yi zargin cewa tun farko gwamnatin jihar ta soma ne da biyansu naira dubu N50,000 ga wasunsu kafin daga bisani lamurra suka canja inda aka koma ana biyansu naira N30,000, batun da suka ce da lauje a cikin nadi.
To sai dai da yake maida martani yayin magana da manema labarai, Kwamishinan harkar noma, na jihar Taraba Mr. David Ishaya ya ce ai dama akan kwantaragi aka dauke su, bisa yarjejeniyar za’a biya mutum ne bisa kwazonsa.
Kawo yanzu dai hadakar kungiyoyin kwadago a jahar ba ta ce komi ba tukunna kan sallamar wadannan ma’aikatan kokumban, yayin da su kuwa ‘yan gwari da su ke wannan sana’ar su ka soma bayyana ra’ayinsu da cewa jama’a sun fi sha’awar na Jos.
Ga Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum