Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Jiragen Sama A Najeriya Sun Ajiye Yajin Aikin Su


Jirgin kamfanin jigilar fasinja na Najeriya.
Jirgin kamfanin jigilar fasinja na Najeriya.

Ma’aikatan sashen sufurin jiragen sama sun kawo karshen yajin aiki da suke yi bayan hana zirga zirgar jiragen kasashen waje a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala International Airport a jiya Litinin.

Ma’aikatan kamfanin kula da ayyukan jiragen sama na Najeriya, NAHCO, sun gudanar da yajin aiki domin kalubalantar batun karin albashi da kuma rashin kula da jin dadinsu duk karin kashi dari bisa dari a kan kudin jigilar jiragen sama.

Wasu hotuna aka kafe a shafukan sada zumunta na zamani a ranar Litinin sun nuna yanda fasinjoji suka makale kana suke cikin damuwa a filin saukar jiragen na Lagos.

Sai dai kungiyar manyan ma’aikatan sashen sufurin jiragen sama ta Najeriya (ATSSSAN) ta yi nasarar kawo karshen yajin aikin.

Babban sakataren kungiyar ta ATSSSAN, Frances Akinjole shine ya fadawa manema labarai batun dakatar da yajin aikin da yammacin jiya Litinin.

Tun da safiyar ranar Litinin ne kamfanin NAHCO mai gudanar da ayyukan jiragen sama a Najeriya ya bayyana nadamarsa ga wannan lamari kana ya yi alkawarin magance batun.

Wasu kwararru a wannan fanni sun ce ya kamata NAHCO ta yi wa ma’aikatan karin albashi koda na kashi 10 cikin 100 ne.

XS
SM
MD
LG