Littafan Luggan harshe Hausa sun taimaka wajen basirar waka
Shirinmu na nishadi a wannan mako ya samu bakwanci wani mawakin fina-finai Ibrahim Ibrahim wanda aka fi sani da Ibrahim Malam.
Ibrahim Malam ya ce ya fara harakar waka ne tun yana dan karami kuma yana samun basirar waka ne ta hanyar yawan karance karance litattafai lugga na harshen Hausa sannan ma’aborin jin wakokin Indiya.
Ya ce kimanin shekaru goma sha biyar kenan yana harkar waka, ko dayake ya soma ne da wakokin fina-finai daga bisani ya tsunduma wakokin nishadi, nanaye da ma na siyasa.
Ibrahim Malam ya ce litattafai kamar na su Aliyu Akilu, wakar Infiraji , da Ma’auzu Hadejia da Modi speaking da Sa’adu Zungur da dai sauransu ne ya ba bashin karsashin yada harshe Hausa da samun karsashin yin waka.
Ya ce saboda jin wakokin Indiya ne ya sa idan yana rera waka ya kan yi amfani da Karin ko salo irin na.
A fannin tsegumi kuwa a makon da muka yi bankwana da ita ne jarumi Ali Nuhu da Rahma Sadau suka leka kasar Nijar inda suka yi wasa domin shagulgulan bukukuwan sallah .