Wannan takaddamar shugabanci ta haifar da baraka wacce ta nuna rarrabuwar kawunan da ke da nasaba da akidar kowannensu, kan yadda kungiyar ke ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi.
A labaranta na mako mako kungiyar IS ta bayyana sunan Abu Musab Al-Barnawi a matsayin wakilinta na Boko Haram.
Sanarwa na IS ba ta yi bayani dalla dalla ba, amma abin lura shi ne akwai alamu da ke nuna cewa an tsige Shekau daga mukaminsa, wanda shi ya ringa jagorantar hare-hare da kungiyar ta rika kaiwa tun daga shekarar 2009.
Rahotannin da Kafar yada labarai ta sahara ta fitar sun ruwaito cewa Al Barnawi shi ma ya fitar da wata sanarwa inda ya ke kalubalantar Shekau.
Wani mutum da ya yi ikrarin cewa shi ne Shekau, ya mayar da martani a wata sanarwa ta faifan sauti mai tsawon minti goma kan juyin mulkin da aka yi wanda aka saka a shafin sadarwa na Youtube kafin daga bisani a cire sautin.
A cikin jawabinsa Shekau ya nanata matsayinsa na daukar ragamar shugabancin kungiyar inda ya ce Al-Barnawi, wanda tsohon mamba ne a kungiyar, na so ne ya haifar da husuma a tsakanin ‘yan kungiyar.