Wasu rahotannin na nuni da cewar Timothy Weah, 'Da ga shugaban kasar Laberiya, George Weah, wanda yake taka leda wa tawagar 'yan kasar Amurka na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta Celtic, a matsayin aro daga kungiyar Paris-saint German.
Sai dai yayin hirarsa da wata kafar watsa labarai Timothy Weah, yace shi har yanzu bai bayyana makomarsaba, har sai ya zauna da 'yan uwansa domin tattaunawa kan wannan lamari na canji sheka a matsayin aro.
Dan wasan ya samu kansa cikin kungiyar PSG ne a watan Agusta, inda ya fafata a wasanni daban daban, wanda suka hada da Super Cup wasansu da Monaco, da kuma wasan farko na Ligue 1 da kungiyar Caen, da Guingamp.
Dan wasan mai shekaru 18 da haihuwa ya fafatawa kasar Amurka a wasanni har guda 8, a wannan shekarar kama daga wasan da sukayi da Paraguay, ya fara jefa kwallon sa na farko a wasan da sukayi da Bolivia.
Timothy Weah, wanda aka haifeshi a birnin New York, ya koma kasar Faransa da taka leda, shekaru hudu da suka gabata inda ake alakantashi da wanda zai gaji mahaifinsa George Weah, wajan lashe gwarzon shekara a bangaren kwallon kafa.
Mahaifinsa ya lashe gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya a shekara ta 1995, inda yanzu ya zama Shugaban kasar Laberiya.
Facebook Forum