Kwamitin shugaban kasa da aka kafa domin yin garanbawul ga rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yakar ‘yan fashi ta SARS, ya amince da tsarin ba jihohi da kananan hukumomi damar kafa rundunonin ‘yan sandansu na kansu.
Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin shugaban hukumar kare hakkin bil Adama, Tony Ojukwu, ya bayyana a cikin shawarwarin da ya bayar cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.
Baya ga batun samar da ‘yan sanda jihar, kwamitin har ila yau, ya ba da shawarar samar da karin kudaden da kayayyakin aiki ga rundunar ‘yan sanda kasar.
Ya kuma nemi da a kara habaka fannin sadarwar rundunar a rahoton da ya gabatarwa shugaba Buhari.
Daya daga cikin masu magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce, ya tabbatar da cewa shugaban Najeriya, ya karbi rahoton kwamitin a yau Litinin.
A cewar Shehu, shugaba Buhari ya ba da umurnin a kafa wani kwamiti mai dauke da mutum uku domin ya yi nazari kan rahoton, ya kuma fitar da matsaya daga karshe cikin watanni uku.
Ko da yake, wasu kafofin yada labarai a Najeriya, sun ruwaito cewa, shugaba Buhari tuni ya ba da umurnin a aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar na samar da ‘yan sandan na jihohi da na kananan hukumomi cikin watanni uku.
Amma a bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu ya ce kore rahotannin.
“Zai zama kamar riga malam masallaci idan aka nuna cewa shugaban kasa ya amince da wani bangare ko daukacin shawarwarin da ke cikin rahoton, ba za a yi hakan ba, har sai an fitar da matsaya ta karshe a rubuce (white paper.)”