Inji kakakin hukumar kwastan ashirye suke su bayyana a gaban kwamitin da'a na majalisar dattawa suyi bayani dalla dalla akan motar da suka kama .
Jami'in labarun hukumar kwastan din Joseph Atta ya musanta dalilin da ya sa shugaban hukumar bai bayyana gaban kwamitin ba don yin bayani akan motar. Hamid Ali bai ki bayyana ba saboda takaddamar dake tsakaninshi da Majalisar akan sanya kayan sarki.
Ita motar dai tun watan Janairu hukumar kwastan ta kamata a Legas saboda wai Sanata Bukola Saraki da aka ce motar tashi ce bai biya harajin Naira miliyan saba'in da hudu ba.
To saidai lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Dr Bukola Saraki ya bayyana a gaban kwamitin ya musanta shigo da motar yana mai cewa Majalisar ce ta sayeta. Yace yawancin motocin majalisar ba za'a san an yi odarsu ba sai an kawosu. Ya nuna motar mallakar Majalisar Dattawa ce.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum