A yayin da Gwamnatin tTarayyar Najeriya ke cewa, shirinta na ciyar da dalibai a wasu daga cikin makarantun firamare na kasar na kara alkaluman daliban da ke zuwa makaranta, masu bibiyar aiwatar da shirin na cewa, wani nau’in abincin da ake baiwa daliban hadarin ga lafiyar su.
Shirin wadda ke karkashin kulawar Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, an fara aiwatar da shine a wasu jihohin kasar a shekara ta 2016.
Baya ga jan hankalin ‘ya'yan masu karamin karfi da su je makaranta, shirin ya samar da ayyukan yi ga masu abinci fiye da dubu 80 a cewar wata sanarwar kakakin mataimakin shugaban na Najeriya.
Wadansu yaran da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana ra’ayoyi da suka yi karo da juna kan shirin ciyar da su abinci, yayin da wasu suka yaba da shirin, wasu kuma sun bayyana cewa, abincin ba shi da dandano kamar irin wanda suke ci a gida.
Yanzu haka dai ana aiwatar da shirin a jihohi 24 daga cikin 36, kodayake, Kano/Jigawa na cikin jihohin da aka fara shirin watanni 4-5 a suka shude.
Hakika wannan tsari ya taimaka wajen zuburar da dalibai su zo makaranta, amma tilas ne masu kirkiro da shirin da kuma aiwatar da shi su sake salo muddin ana muradin nasara, a cewar wasu malaman firamare da suka bukaci Muryar Amurka kada ta bayyana sunayensu.
Malama Ilham Sale, daya daga cikin wadanda ke kwangilar dafa abincin a jihar Kano ta bayyana cewa, an basu zabin yadda za su raba abincin, ko dai su sayi kwanonin da za su rika wankewa ko kuma su raba a robobin da yara za su tafi da su. Tace ta zabi sayen robobin da zata rika wankewa domin rage kashe kudi.
Sai dai Comrade Yahya Shu’aibu Ungogo da ke bibiyar yadda ake aiwatar da shirin ciyarwar a wasu sassan jihar Kano ya ce, koda yake tsarin yana da kyau a rubuce, amma yana neman zama barazana ga lafiyar dalibai.
Yace akwai bukatar hukumar tantance ingancin abinci da hukumar lafiya da kuma masu ruwa da tsaki su sa ido sosai kan irin abincin da ake kai wa makarantun domin kada ana neman kiba, a rame.
Bisa ga cewarsa, idan ba a yi kyayyawar kulawa ba, yaran suna iya kamuwa da wadansu cututtuka ko kuma abincin ya zama sanadin wata lalura da za su iya fama da ita iya rayuwarsu.
Hukumar kula da da’ar al’umma wato CRC ta gwamnatin jiha ita ce ke kula da aiwatar da shirin a nan jihar Kano, amma kokarin da wakilinmu a birnin Kano ya yi domin jin ta bakin shugabannin hukumar kan wannan batu ya ci tura.
Ga cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum