Yanzu haka dai rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta kama wasu da ake zargin suna da hanu a hargistin da ya auku a Jalingo fadar jihar, biyo bayan bada sakamakon zaben gwamnan jihar, lamarin da ya jawo asarar rayuka.
Kawo yanzu ana samun tashe tashen hankula a wasu wuraren, yayin da aka kara tura jami’an tsaro domin kare rayuka.
Ya zuwa safiyar wannan rana ta Laraba, ana cikin zaman dar-dar a fadar jihar, kuma duk da matakan tsaron da aka dauka akan kaiwa juna hari kamar yadda ya faru a anguwar Saminaka da kuma kauyen Tau.
Shi dai dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Sani Abubakar Danladi, kira yayi ga magoya bayan sa da su kwantar da hankulansu.
Rundunan 'yan sandar jihar Taraban ta bakin kakakinta ASP David Misal, tace tuni aka kama wasu da ake zargi.
Ga rahoton wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Ibrahim Abdul’Aziz.
Facebook Forum