Ana sa ran kungiyoyin masu hamaiya a jamhuriyar Congo karkashin laimar kungiyar Rassemblement, zasu koma teburin shawarwarin samun zaman lafiya da gwamnatin kasar a makon gobe idan Allah ya kaimu duk da mutuwar shugaban kungiyar Etienne Tshisekedi.
Magoya bayan masu hamaiya da kungiyoyin jama’a sun baiyana damuwar cewa mutuwar Etiene Tshisekedi zata gurgurta yarjejeniyar da aka kula da gwamnati a kwanan nan.
Yarjejeniyar ta tanadi harda barin shugaba Joseph Kabila ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya na tsawon shekara guda, sa’anan sai ayi zabe.
Freddy Mbuyamu Matungulu shugaban jam’iyar Nabiso ta masu hamaiya yace ana sa ran shugabanin cocin Katolika masu shiga tsakani wadanda suka dakatar ko kuma suka jingine shawarwari tsakanin gwamnati da kungiyar Rassemblement, zasu koma birnin Kinshasa domin tada injin din shawarwarin.