Da ya ke amsa tambayoyi daga Halima DJimrao, Dr Manga ya ce idan mutun ya san matsayinsa game da wannan cutar, to ko da an same shi da ita, akwai fa'ida sosai saboda idan aka fara shan magani da wuri za a iya cin karfin cutar har da kashi 90%. Don haka ya ce za su yi kokarin gwada mutane akalla dubu shida (6,000). Ya ce za su yi amfani da kayan fadakarwa sosai don ganar da jama'a.
To amma Dr. Manga ya ce an sami cigaba sosai a yakin da ake da cutar saboda cutar ta ragu zuwa 2.1% daga yadda ta ke a 6.8% a shekara ta 2001 a jihar ta Bauchi. Ya ce a matakin Tarayya ma an sami saukin cutar saboda ta ragu zuwa kashi 4%. Dr. Manga ya ce za su dau sati guda su na yekuwar yaki da cutar da kuma nuna ma mutane muhimmancin nuna kauna da kulawa ga masu dauke da cutar a maimakon
nuna masu kyama.