Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta daukaka kara kan Jan katin da aka ba wa dan wasanta Son Heung, a wasan da su kayi da Everton ranar Lahadin da ta gabata a gasar firimiyar Ingila.
Alkalin wasan da ya hura Martin Atkinson, ya bada katin ne bayan da a kayi arangama da dan wasan Everton Andre Gomes, lamarin da ya haifar da munmunar rauni a idon sahunsa (Ankle injury).
Inda wasu 'yan wasa hankalinsu ya tashi yayin da suka ga wannan rauni wanda sai da aka tsayar da wasan na tsawon minti shida kafin daga bisani aka ci gaba.
Sai dai a ranar litinin da ta gabata a kayi wa dan wasan Gomes, tiyata a kafarsa ta dama inda ya samu raunin.
Kocin Tottenham Mauricio Pochettino, yace dalilin daukaka karar shine dan wasan nasu Son Heung- bai aikata wannan lamari cikin ganganciba, domin a bayyane yake kuma bai cancanci a bashi Jan katiba.
In har Kungiyar batayi nasara akan daukaka kararbar ba, Son ba zai buga wasanni uku da Tottenham zata buga ba da suka hada da wasansu da Sheffield United, West Ham da kuma Bournemouth ba a gasar firimiya lig na bana.
Amman idan kungiyar tayi nasara to za'a sassauta wannan hukuncin.
Facebook Forum