Tawagar wakilan Afghanistan fiye da 50 suka kammala wani babban taro da ‘yan kungiyar Taliban jiya Litinin, inda suka fidda wata sanarwar hadin gwiwa dake jaddada bukatar kawo karshen kisan fararen hular da ake yi a yakin basasar kasar, da kuma cimma kyakkyawar matsaya a zaman shawarwarin neman sulhun da ake yi tsakanin ‘yan kungiyar Taliban da Amurka a birnin Doha.
Sun kuma jaddada muhimmancin kawo duka bangarorin a zaman tattaunawar da ake yi don kawo karshen yakin da ya kwashe shekaru 18 ana yi a kasar.
“Duka wadanda suka halarci taron gaba dayansu sun amince da cewar an cimma cikakken, dorarren zaman lafiya, abinda jama’ar Afghanistan ke bukata, zai iya yiwuwa ne kawai idan shawarwarin da ake yi ya hada duka bangarorin, a cewar sanarwar.”
An dai yabawa Taron da aka yi a matsayin na tarihi wanda karon farko ya hada da jami’an gwamnatin Afghanistan, ko da yake don kansu suka je. A baya, kungiyar Taliban ba ta amince ta tattauna kai-tsaye da wasu wakilan gwamnati ba, tana kuma yiwa gwamnatin Afghanistan kallon wadda bata dace ba a hukumance kuma ‘yar amshin Amurka.
Facebook Forum