Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar OPEC Ta Amince da Rage Man Fetur da Kasashenta Ke Hakowa


 Saleh Al-Sada, Shugaban OPEC a tsakiya, Baban Sakataren OPEC Mohammed Barkindo,
Saleh Al-Sada, Shugaban OPEC a tsakiya, Baban Sakataren OPEC Mohammed Barkindo,

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetir ta OPEC jiya Laraba ta amince zata rage yawan man da kasashen ke hakowa, a karon farko tun cikin shekara 2008, a wani kokarin bunkasa parashi da kuma kalubalantar sauran kasashen da basu cikin kungiyar su bi sahu.

Ministan mai na Iran yace kungiyar zata rage yawan man da take hakowa da kimanin garwa miliyon daya da dubu dari biyu. Yanzu zasu dinga hako miliyon 32 da dubu dari biyar ne a kowace rana. Ragin ya na kwatankwacin kimamin kashi daya daga cikin dari na dukkan man da kasashen ke hakowa.

Kafin ayi taron na jiya Laraba a birnin Vienna, ministan makamashin Saudiya yace kungiyar OPEC zata bukaci kasashen da basu cikinta su rage yawan man da suke hakowa.

Kasar Rasha, wadda bata cikin kungiyar ta OPEC ta amince da rage yawan mai da take hakowa da ganga dubu dari uku a kowace rana.

Kungiyar ta OPEC tace tana so taga parashin mai a duniya ya koma tsakanin dola 55 zuwa dolla 60 ganga guda, matsayin da tace zai farfado da tattalin arzikin kasashen da suka dogara akan man fetir, wanda kuma suka yi shekaru biyu suna shan wahala sakamakon faduwar parashin man zuwa kasa da dalla hamsin ganga guda.

Wannan labari daga kungiyar OPEC da Rasha yasa farashin mai tashi da kashi 10 a kasuwar birnin New York kuma ya bunkasa farashin hanayen jarin makamashi.

Farashin mai ya tashi daga dola 4.29 zuwa dola 49 da kwabo arba’in da hudu ganga guda jiya Laraba.

XS
SM
MD
LG